Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kara ba da iznin zuba jarin waje a fannoni 7 na kasuwar kasar
2019-07-01 14:49:47        cri

Sabuwar takardar bayanin da kasar Sin ta fitar game da sassan da baki ba za su zuba jari ba ta shekarar 2019, na nuna cewa, daga ranar 30 ga watan Yuli, za a rage ko soke wasu sassan da baki ba za su zuba jari ba a fannonin da suka shafi harkokin jiragen ruwa, gas da ake amfani da shi a birane, sinima, hukumomi dake dillancin nuna shirye-shirye, da karin harkoki a fannin sadarwa, bincike da hako iskar gas da man fetur da dai sauransu. Kwararru sun bayyana cewa, wannan mataki da kasar Sin ta dauka ya nuna cewa, kasar Sin na kokarin kara bude kofa ga kasashen ketare, ya kuma biya bukatun kasashen ketare a wannan fannin

Kasar Sin na tafiyar da tsarin nuna matsayin daidaito ga jarin waje kafin su soma zuba jari da sassan da baki ba za su iya zuba jari ba bisa wannan takardar bayani na sassan da baki ba za su zuba jari ba. Duk jarin waje da takardar ba ta shafa ba, za su kasance daya da kamfanonin kasar Sin. Sabuwar takardar da kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin da ma'aikatar kasuwancin kasar suka fitar a ranar 30 ga watan Yuni, ta rage sassan da baki ba za su zuba jari a ciki ba daga 48 zuwa 40, kana a cikin takardar sassan da baki ba za su zuba jari ba a fannin yankunan gwaji na cinikayya cikin 'yanci da aka bayar a wannan rana, an rage sassan daga 45 zuwa 37.

Game da haka, daraktan sassan jami'ar YNU ta kasar Japan dake nan birnin Beijing, Liu Qingbin yana ganin cewa, matakin da kasar Sin ta dauka ya nuna cewa, kasar na kokarin gaggauta bude kofa ga kasashen ketare. Ya ce,

"Matakin kaddamar da takardar sassan da baki ba za su zuba jari ba, da sabuwar takardar da aka fitar, sun nuna cewa, kasarmu na kokarin kaiwa matsayin kasa da kasa, ban da wannan kuma, sun nuna cewa, muna kara gaggauta bude kofa ga kasashen ketare. Musamman ma a fannin sadarwa dake amfani da fasahar 5G, wanda ke samun bunkasuwa a kasashen duniya, kasar Sin ta bude kofa ga kasashen ketare a wannan fannin, gaskiya tana kan gaba a duniya wajen bude kofarta."

Bisa wannan sabuwar takarda, kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasashen ketare a fannin ba da hidima, wanda ya jawo hankulan mutane sosai. A ganin Liu Qingbin, bude kofa a fannin al'adu, shi ma ya nuna cewa, kasar Sin na kara imani a fannin al'adu. Ya ce,

"Bude kofa zai inganta yin takara, ta yadda za a ciyar da sana'o'i gaba yadda ya kamata. Za mu shigar da kayayyakin al'adu na kasashe daban daban cikin kasarmu, wannan ya nuna cewa, muna kan gaba a duniya a wannan fannin. Baya ga haka, ba kawai yadda bude kofa zai nuna imanin da muke da shi a fannin al'adu ba, har ma zai wadatar da al'adun kasarmu."

A cikin wannan sabuwar takardar da aka fitar, an kaddamar da sabbin matakan bude kofa ga kasashen ketare a fannonin ba da hidima, kere-kere, hakar ma'adinai da aikin gona, kana an amince jarin waje su samu 'yancin tafiyar da harkokin wani kamfani ta hanyar mallakar wani kason hannayen jari ko gudanar da harkoki da zuba jari shi kadai, da kara matakan gwaji a yankunan cinikayya cikin 'yanci na gwaji, da kuma kafa yanayin zuba jari mai salon bude kofa da sauki da kuma adalci, da inganta hadin kan jerin sana'o'i a tsakanin kasa da kasa.

Mataimakin shugaban sashen nazarin kasuwannin duniya na kwalejin nazari na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, Bai Ming ya bayyana cewa, idan aka takaita sassan da baki za su zuba jari, hakan zai karawa sassan daraja, da kuma kara nuna imanin da kasar Sin ke da shi. Bai Ming ya ce,

"An sha takaita sassan da baki za su zuba jari, kuma idan aka takaita sassan, hakan zai karawa sassan daraja, kana ana gani cewa, kasarmu ta samu ci gaba a fannin shari'a da dokokin da abun ya shafa. Matakin da kasar Sin ta dauka na kara habaka sassan ba da izni ga jarin waje na shiga kasuwarta, ya biya bukatun kasashen ketare na kasar Sin. Kamar yadda aka gani, kasar Sin ta dauki duk wadannan matakan bude kofa ne, bisa radin kanta. A sa'i daya kuma, mun gano cewa, kara bude kofa ga kasashen ketare, zai amfanawa kasar Sin wajen kara karfinta na fada a ji kan tafiyar da harkokin tattalin arziki a dandalin duniya, kana zai kara imanin kasar Sin wajen tinkarar takaddamar cinikayya a nan gaba."

Kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya bayyana cewa, an fitar da takardar sassan da baki ba za su zuba jari ba ta shekarar 2019, a matsayin wani muhimmin matakin da kasar ta dauka na kara bude kofa ga kasashen ketare a sabon yanayin da ake ciki. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China