Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mozambique da Sin na kara daukaka dadaddiyar dangantakarsu
2019-07-12 15:19:38        cri

An gudanar da wani taron karawa juna sani game da dangantakar kasashen Sin da Mozambique, jiya Alhamis a birnin Maputo, domin karfafa aminci da dangantaka da kara yaukaka daddadiyar zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.

Manyan jami'an gwamnati da malamai da kwararru da wakilan dalibai ne suka halarci taron, inda tsohon shugaban kasar Mozambique Joaquim Chissano, ya ce wasu mutane ba su aminta da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ba, amma a ganinsa, kasar Sin ta shirya hadin gwiwar ne bisa gaskiya. Ya ce muddun 'yan Afrika suka rungumi akidu da burikansu, to za su cimma muradinsu ta hanyar shiga shawarar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China