Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci a shigar da matasa cikin yaki da ta'addanci
2019-07-12 09:33:05        cri

Wakiliyar AU dake kula da harkokin matasa Aya Chebbi, ta ce akwai bukatar kasashen Afrika su yi amfani da karfi da basirar matasa wajen karfafa yaki da tsattsauran ra'ayi da ya samu wurin zama, yayin da ake tsaka da fama da talauci da rikice-rikice da take hakkokin al'umma.

Aya Chebbi ta ce nasarar shirye-shiryen yaki da ta'addanci a Afrika, ta dogara ne kan kara damawa da matasan nahiyar wajen tsara manufofi da wayar da kansu kan matsalar.

Ta bayyana a gefen taron yaki da ta'addanci na Afrika dake gudana a birnin Nairobin kasar Kenya cewa, ya kamata gwamnatocin nahiyar su sauya manufofin dake kin shigar da matasa cikin harkokin shugabanci da tsara manufofi, domin tabbatar da sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya da tsaro da kare tsattsauran ra'ayi.

Aya Chebbi mai shekaru 31 'yar asalin kasar Tunisia, mai rajin tabbatar da zaman lafiya, ta ce taron na nahiyar kan yaki da ta'addanci, ya samar da damar tattauna kara shigar da matasa cikin yaki da matsalar da ke haifar da koma-baya ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaban nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China