Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gabon ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin AU 3
2019-07-07 16:05:15        cri
A ranar Asabar kasar Gabon ta sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi 3 na kungiyar tarayyar Afrika (AU) bayan da AU din ta yi kira ga mambobinta da su kara azama wajen amincewa da yarjejeniyoyin nahiyar.

Jamhuriyar Gabon ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin 3 ne a gefen babban taron kolin kungiyar karo na 12 na shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen mambobin AU, wanda aka bude a ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli a Niamey, babban birnin jamhuriyar Nijer.

Yarjejeniyoyin uku wadanda kasar ta tsakiyar Afrika ta sanyawa hannu sun hada da yarjejeniyar AU ta hadin gwiwar kan iyakoki, da yarjejeniyar Afrika ta kare hakkin bil adama ta bangaren 'yancin tsofaffi sai kuma yarjejeniyar Afrika ta kare hakkin bil Adam ta bangaren hakkin masu nakasa.

Matakin sanya hannun kan yarjejeniyoyin AU uku da kasar Gabon tayi ya zo ne bayan wani gargadin da kungiyar ta Afrika ta yiwa kasashen cewa rashin sanya hannu kan yarjejeniyoyin nahiyar Afrika suna haifar da koma baya ga yunkurin tabbatar gina dauwamamman cingaban al'ummar kasashen Afrika.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China