Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin kasashen wajen Afrika za su yi taro kan yarjejeniyar cinikin maras shinge
2019-06-20 09:30:15        cri
A farkon wata mai zuwa ministocin harkokin wajen kasashen Afrika za su yi taro a Niamey, babban birnin jamhuriyar Nijer domin tattauna yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar cinikin masar shinge na Afrika wato (AfCFTA), gabanin taron kolin shugabannin kasashen Afrikan, kungiyar tarayyar Afrika (AU) ce ta bayyana hakan.

Ministocin harkokin wajen kasashe mambobin AU 55, a taron majalisar zartaswar AU da za su gudanar a ranar 4 zuwa 5 ga watan Yulin a Niamey, ana sa ran za su bayar da shawarwari game da yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar ciniki maras shinge gabanin taron kolin shugabannin gwamnatocin AU karo na 12 wanda za'a gudanar a ranar 7 ga watan Yuli, in ji sanarwar AU.

Shugaban gudanarwar kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat ya ce, yarjejeniyar AfCFTA ta kasance a matsayin wani muhimmin ginshiki na burin da AU ke da shi wajen cimma nasarar bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar nahiyar Afrika.

Yarjejeniyar ta AfCFTA, wacce kasashen Afrika 44 suka rattaba hannu a lokacin kaddamar da ita a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, a watan Maris na shekarar 2018, tana fatan ganin an samar da wani tsarin cinikin bai daya a nahiyar ba tare da sanya kudaden haraji ba da nufin bunkasa harkokin kasuwancin kasashen, da bunkasa harkokin cinikayya a tsakanin kasashen Afrika, da bunkasuwar masana'antu da samar da guraben ayyukan yi. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China