Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci kasashen Afirka da su dauki matakan kare yara daga cin zarafi da bautarwa
2019-05-15 10:16:21        cri
Kungiyar hadin kan Afirka ta AU, ta nuna matukar damuwa game da karuwar yaran dake tserewa muhallan su a sasan nahiyar daban daban, tana mai fatan za a dauki karin matakan ba da kariya ga yara kanana daga cin zarafi da bautarwa.

Wata sanarwa da majalissar kungiyar mai lura da zaman lafiya da tsaro ko AU-PSC ta fitar, ta ce sakamakon taron baya bayan nan da aka gudanar game da wannan kalubale, AU-PSC na fatan daukacin kasashe mambobin AU dake fama da tashe tashen hankula, za su dauki kwararan matakai na tabbatar da biyayya ga dokokin kare hakkokin jin kai na bil Adama, musamman ma tabbatar da cewa yaran da suke zuwa makaranta sun samu kariya daga hare haren soji.

Sanarwar ta kara da cewa, ya zama wajibi a gano tushen fadace fadace dake jefa yara cikin mummunan yanayi a wasu sassa na nahiyar Afirka, domin hakan ya samar da zarafi na gaggauta lalubo dabarun siyasa na magance su, kana hakan zai ba da damar kare yara daga fadawa mawuyacin halin bautarwa da shigar da su ayyukan soji.

A kwanakin baya ne dai AU-PSC ta gudanar da wani taro mai take "yara da yake-yaken sojoji ke shafar rayuwar su a nahiyar Afirka", a wani mataki na zakulo dabarun magance wannan matsala. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China