Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afrika na yin taro game da bunkasa kwarewa
2019-06-20 10:05:52        cri
Kimanin kasashen Afrika 15 ne suke gudanar da taron kwanaki uku wanda aka bude daga ranar Laraba a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu domin tattaunawa game da yadda za'a kara inganta shirin bada horo ga matasa don rage matsalolin rashin ayyukan yi a tsakanin matasan da bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika.

Taron wanda kungiyar raya cigaban kasashen Afrika (AUDA-NEPAD) ta shirya, wanda ta kunshi gwamnatocin kasashen Afrika, da kungiyoyin hulda na kasa da kasa da hukumomi masu zaman kansu.

Estherine Fotabong, shugabar shirin AUDA-NEPAD, ta ce, samar da horo da kuma kwarewa kan ilmin sana'o'i wato (TVET), za'a yi amfani da shi a matsayin wani muhimmin ginshikin da zai taimakawa bunkasuwar kwarewa ga masana'antun kasashen Afrika.

Ta bukaci gwamnatocin kasashen Afrika da su tabbatar da baiwa matasa tallafi don samar musu da ingantaccen yanayi, da kudaden bunkasa sana'o'i. Fotabong ta kara da cewa, kamata ya yi a samar da wani yanayin bai daya, a matakan shiyya da kuma na nahiyar, domin samar da karin damammaki ga matasa daga dukkan bangarori. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China