Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci 'yan kasashen waje su guji yin shisshigi kan harkokin cikin gidan Sudan
2019-06-09 15:38:49        cri
A jiya Asabar kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta bukaci 'yan kasashen waje da su nesanta kansu daga yin katsalandan kan harkokin cikin gidan Sudan a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsanancin rikicin siyasa da rashin tabbas.

Shugaban gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, shi ne ya yi kiran a jiya Asabar, inda ya nanata bukatar Sudan ta dauki matakan warware dambarwar siyasar da ya dabaibaye kasar wanda ke cigaba da dagula al'amurra a kasar.

"Kungiyar AU ta jaddada yin kira ga dukkan 'yan kasashen waje da su guji yin shisshigi, kuma su goyi bayan kungiyar ta AU a kokarin da take na neman lalibo hanyar warware rikicin siyasar kasar ta Sudan kuma su mutunta duk wani mataki da ya shafi muradun al'ummar kasar Sudan, da shiyyar, da ma nahiyar Afrika baki daya," AU ce ta sanar da hakan a jiya Asabar.

Shugaban kungiyar ta Afrika mai mambobin kasashe 55, ya bukaci dukkan bangarorin kasar Sudan da su dauki muhimman matakan siyasar da suka dace, da kuma matakan tsaro da ake bukata, domin bude kofar ci gaba da tattaunawar sulhu da nufin cimma nasarar mika mulki ga gwamnatin farar hula a kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China