2019-06-21 11:10:11 cri |
Jiya Alhamis babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bukaci a kai zuciya nesa bayan da Iran ta harbo jirgin Amurka marar matuki.
Kakakin Guterres, Stephane Dujarric ya bayyana ga 'yan jaridu, cewar "ya nuna damuwa matuka game da abin da ya faru a 'yan kwanakin nan, game da harbo jirgin marar matuki."
Ya kara da cewa, "Ya kamata dukkan bangarorin su kai zuciya nesa kuma su guji aikata duk wani abin da ka iya lalata yanayin da ake ciki a halin yanzu".
Ya ce, mista Guterres ya yi gargadin a guji haddasa duk wani tashin hankali, ya jaddada cewa, duniya ba za ta iya jure yanayi na tashin hankali ba.
Iran ta ce jirgin marar matuki, samfurin RQ-4A Global Hawk, ya saba dokar kasa da kasa ta sararin samaniya, yayin da gwamnatin Amurka ta ce jirginta yana shawagi ne a manyan tekunan kasa da kasa a daidai lokacin da Iran din ta harbo shi a ranar Alhamis.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China