Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Jamus ya yi kira da a kiyaye yarjejeniyar nukiliya ta Iran
2019-06-11 13:58:38        cri
Ministan harkokin waje na kasar Jamus Heiko Maas, ya ce yarjejeniyar nukiliya ta Iran na da matukar muhimmanci, wadda ke bukatar sassa daban daban su kiyaye ta, kuma ya kamata a tabbatar da moriyar Iran bisa ga yarjejeniyar.

Heiko Maas, ya bayyana hakan ne jiya Litinin a birnin Tehran, yayin ziyarar yini daya da ya kai kasar ta Iran, inda ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Iran Mohammad Javad Zarif.

A gun taron manema labarai da aka kira bayan shawarwarin, Maas ya ce, kasancewarsu kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, Jamus, da Faransa, da Ingila, za su tsaya tsayin daka kan kiyaye yarjejeniyar, tare kuma da taimakawa Iran cimma moriyar tattalin arziki kamar yadda yarjejeniyar ta tanada, yayin da ita ma kungiyar tarayyar Turai ke ci gaba da wannan kokari.

Maas ya kara da cewa, kasashen Turai na fatan kara habaka yarjejeniyar cinikayya tare da Iran bisa tsarin INSTEX, suna kuma fatan ganin karuwar tattalin arzikin Iran bisa ga hakan.

A nasa bangaren, Mohammad Javad Zarif ya ce, a halin da ake ciki yanzu, babu damar gudanar da tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China