Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya gana da shugaban bankin duniya
2019-06-11 20:30:37        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugaban bankin duniya David Malpass a yau Talata a nan birnin Beijing. Inda Mista Li ya jaddada cewa, a matsayin mai aiwatarwa, mai bunkasuwa, kuma mai ba da gudunmawa ga tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa a yauzu, kasar Sin tana fatan zurfafa hadin kai da bankin duniya, don ciyar da bunkasuwar duniya mai wadata gaba tare.

Mista Li ya ce, Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, tana kuma fatan sauke nauyin dake wuyanta a duniya, lokacin da take kokarin neman ci gabanta.

A nasa bangare, Malpass ya ce, bankin na fatan zurfafa hadin kai da kasar Sin, da ma duk fadin duniya a fannoni daban-daban.

An ba da labari cewa, Malpass ya zama shugaban bankin na 13, a ran 9 ga watan Afrilun bana, inda zai yi aiki na wa'adin shekaru 5. Wannan ziyara ita ce ta farko da Mr. Malpass ya gudanar a kasar Sin, tun bayan da ya kama aiki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China