Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da daukar kamfanonin cikin gida da masu jarin waje daidai da juna
2019-05-23 19:44:32        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasar na maraba da kamfanonin waje daga dukkanin sassan duniya, ciki hadda kasar Singapore, da su shigo Sin su fadada zuba jarin su, domin kuwa Sin din za ta ci gaba da daukar kamfanonin cikin gida da masu jarin waje daidai da juna.

Li ya bayyana hakan ne, yayin ganawarsa da mataimakin firaminista, kana ministan kudin kasar ta Singapore Heng Swee Keat a nan birnin Beijing. Ya ce Sin a shirye take da ta daidaita shawarar nan ta "ziri daya da hanya daya" tare da manufofin ingiza ci gaban Singapore, da kara zurfafa kawancen hadin gwiwar sassan biyu a fannin cinikayya, da zuba jari, da hada hadar kudade, da samar da birane na zamani da dai sauran su.

Li Keqiang ya kara da cewa, manufar Sin ta kara bude kofa ga sassan duniya ba kawai za ta amfani Sinawa ba ne kadai, a'a manufa ce ta samar da damammaki na ciyar da daukacin kasashen duniya gaba.

A nasa tsokaci kuwa, Mr. Heng ya taya Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin ta zamani. Yana mai cewa, Singapore na da burin zurfafa dadaddiyar dangantakar hadin gwiwa tare da Sin a dukkanin fannoni, musamman a sassan da za su taka rawar gani, wajen inganta alakar Sin da sauran kasashe mambobin kungiyar hadin kan yankin kudu maso gabashin Asiya ko ASEAN a takaice. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China