Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin kula da harkokin raya kasa na kasar Sin ya ba da rancen kudi har dalar Amurka biliyan 3 ko fiye a Afirka
2019-07-01 19:41:27        cri

Wasu rahotanni daga bankin kula da raya kasa na kasar Sin, sun nuna cewa, ya zuwa yanzu bankin ya hada hannu da hukumomin hada-hadar kudi na nahiyar Afirka guda 40, tare da ba da rancen kudi da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 3.2 baki daya.

Bankin kula da harkokin raya kasa na kasar Sin, ya ba da jagoranci wajen kafa kawancen hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka, ta fuskar hada-hadar kudi a watan Satumban shekarar 2018, wanda mambobinsa suka hada da bankin kula da harkokin raya kasa na kasar Sin, da hukumomi 16 na hada-hadar kudi na Afirka, wadanda suke wakiltar nahiyar, kuma suke yin babban tasiri a nahiyar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China