Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kafa sashen sada zumunta tsakanin Sin da Afirka karkashin shugabancin CPPCC
2019-06-19 20:22:16        cri

Yau Laraba ne majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC, ta kafa sashen sada zumunta tsakanin kasashen Sin da na nahiyar Afirka, tare da gudanar da cikakken taron sashen karo na farko. Shugaban CPPCC Wang Yang ya gana da mambobin sashen.

A yayin ganawar, Wang Yang ya yi nuni da cewa, sashen sada zumunta tsakanin Sin da Afirka, ya zama na farko cikin majalisar CPPCC, wanda kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya yarda da kafuwarsa. Don haka dole ne ya yi kokarin ba da gudummowa, wajen aiwatar da sakamakon da aka samu yayin taron koli na Beijing, na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kuma kara raya al'ummar mai kyakkyawar makoma ga dukkan jama'ar Sin da Afirka. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China