Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da hanyar jiragen sama zuwa Afirka kai tsaye ta farko a lardin Hunan na kasar Sin
2019-06-12 14:12:15        cri
A yau da karfe 1 na dare, jirgin sama na farko na kamfanin China Southern Airlines daga birnin Changsha na Sin zuwa Nairobi na kasar Kenya ya tashi daga filin jiragen saman Changsha. Bayan shafe awoyi 11 da mintoci 30, jirgin saman dake dauke da fasinjoji fiye da 200 zai isa filin jiragen saman Nairobi na kasar Kenya. Wannan ne hanyar jiragen sama ta farko dake tsakanin birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin zuwa nahiyar Afirka.

An ce, kasar Kenya muhimmiyar kasar Afirka ce dake bin shawarar "ziri daya da hanya daya", babban birnin kasar wato Nairobi shi ne cibiyar tattalin arziki da watsa labaru a yankin gabashin Afirka. Bayan da aka bude hanyar jiragan saman, za a samar da sauki ga jama'ar kasashen biyu da suka yin tafiye-tafiye ta hanyar jirgin sama, kana za a sa kaimi ga raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin lardin Hunan da kasashen Afirka, ta hakan za a taimaka wajen samun ci gaban hadin gwiwa da samun moriyar juna a tsakanin Sin da Afirka. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China