Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta gudanar da taro kan tsaro da zaman lafiya na farko tsakaninta da kasashen Afrika
2019-06-28 10:20:59        cri

Ma'aikatar kula da harkokin tsaro ta kasar Sin za ta gudanar da taro kan tsaro da zaman lafiya na farko tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, daga ranar 14 zuwa 20 ga watan Yuli.

Kakakin ma'aikatar Ren Guoqiang, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, wadanda za a gayyata domin halartar taron sun hada da jami'an dake aiki a sassan dake kula da harkokin tsaro na kasashen Afrika da jami'an soja da wadanda ke kula da shirye-shiryen tabbatar da tsaro da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afrika.

Ya kara da cewa, tattaunawar da za a yi yayin taron, za ta mayar da hankali kan samar da al'umma mai aminci da makoma guda ga Sin da Afrika, da kuma maudu'an da suka hada da yanayin tsaro a nahiyar da muhimman batutuwan yankuna da hadin gwiwar Sin da Afrika ta fuskar tabbatar da tsaro da zaman lafiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China