Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gogewar kasar Sin a fannin ci gaba ka iya zama misali ga nahiyar Afrika
2019-06-27 12:23:09        cri

Tsohon babban mataimakin shugaba kuma babban masanin harkokin tattalin arziki na Bankin Duniya Justin Yifu Lin, ya ce gogewar kasar Sin a fannin ci gaba zai iya zama abun misali ga kasashen Afrika, la'akari da yadda suke neman raya kansu da yaki da talauci.

Justin Yifu Lin, ya bayyana haka ne a jiya, gabanin taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya da ake tsakanin Sin da Afrika a karon farko.

Jami'in wanda kuma masanin harkokin tattalin arziki ne a Jami'ar Peking ta kasar Sin, ya ce kasar Sin na daya daga cikin matalautan kasashe a duniya a shekarun 1970, amma ta tashi zuwa kasa ta biyu, mafi karfin tattalin arziki a duniya ta hanyar aiwatar da gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje.

Ya ce dabarar tafiya da zamani ta kasar Sin ta samar da sabon zabi ga kasashen Afrika dake neman samun ci gaba da kare cikakken 'yancinsu a lokaci guda.

Ya ce taron baje kolin cinikayya da ake gudanar a birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin, zai yayata gogewar Sin da Afrika a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, yana mai cewa, za a gabatar da daftarin dake kunshe da bayanai 101, kan batutuwan da suka hada da harkokin noma da ayyukan masana'antu da kasuwanci da cinikayya da makamashi da hadin gwiwa a yankin masana'antu da gine-gine da aikin injiniya da hada-hadar kudi da hidimomi, ga mahalarta taron.

Ya ce masana'antun sarrafa kayayyakin fitarwa kasashen waje dake samun tagomashi da yankin masana'antun kasar Sin ta zuba jari ya ingiza, ya sanya Habasha zama kasa mafi dacewa ta zuba jarin waje, yana mai cewa, kasashen Afrika za su iya shiga cikin harkokin dunkulewar tattalin arzikin duniya da irin na su salon fa'idojin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China