Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Sin da Afirka sun yi kira ga kasashen Afirka da su yi amfani da damar dake tattare da shawarar "ziri daya da hanya daya"
2019-05-25 16:35:06        cri

Masanan kasashen Sin da Afirka, sun yi kira ga kasashen Afirka da su yi amfani da kyakkyawar damar dake tattare da shawarar "ziri daya da hanya daya" wajen bunkasa kasa.

Masanan sun fadi haka ne jiya Jumma'a, yayin taron dandalin tattaunawa tsakanin masanan Sin da Afirka a Lusaka, babban birnin kasar Zambia.

Pamela Kabaso, darektar zartaswa ta kwalejin nazarin manufofin ta Zambia, ta yi nuni da cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta samar wa kasashen Afirka dabarun daidaita batutuwan raya kasa. Ta ce hada shawarar da manyan tsare-tsaren bunkasa yankin ciniki cikin 'yanci na Afirka, zai kara azama kan ci gaban Afirka.

A nata bangaren, Liu Haifang, mataimakiyar shehun malama a kwalejin nazarin huldar kasa da kasa ta jami'ar Peking ta kasar Sin, ta ce, alkaluma sun nuwa cewa, idan kasar Sin na kera kaya a kasashen ketare, to ayyukanta za su samar da guraben aikin yi miliyan 70 a kasashen. Shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta samar wa kasashen Afirka kyakkyawar damar raya kasa, amma dole sai kasashen sun shiga aikin aiwatar da shawarar, in ba haka ba, ba za su ci gajiyar ta ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China