Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattaunawar shugabannin Sin da Amurka ta ja hankalin duniya
2019-06-30 16:22:13        cri

Shugabannin kasashen Sin da Amurka sun tattauna a jiya Asabar, a birnin Osakan kasar Japan, a yayin da aka gudanar da taron koli na kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki wato G20, tattaunawar da ta ja hankalin kafofin yada labaru na kasa da kasa sosai.

Manyan kafofin yada labaru na Amurka ciki hadda The Washington Post da The New York Times da dai sauransu, sun ba da labari kan tattaunawar shugabannin Sin da Amurka nan da nan ba tare da bata lokaci ba kan shafukansu na farko. Sa'an nan kuma, 'yan kasuwar Amurka sun yi maraba da daidaiton da shugabannin 2 suka cimma.

Har ila yau manyan kafofin yada labaru na kasashen Faransa, Argentina, Chile da sauran kasashe sun ba da labaru kan tattaunawar shugabannin Sin da Amurka da kuma kudurinsu na maido da shawarwari tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da ciniki. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China