Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya gana da Putin da Modi
2019-06-28 20:28:57        cri

A yau Jumma'a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da firayin ministan kasar Indiya Narendra Modi a birnin Osakar kasar Japan, inda shugabannin uku suka yi musanyar ra'ayoyi, game da yanayin da kasashen duniya ke ciki yanzu, da muhimman batutuwan kasa da kasa, da na shiyya shiyya, tare kuma da hadin gwiwa tsakanin sassan uku.

Yayin ganawar ta su, baki daya shugabannin uku sun yarda cewa, za su ci gaba da karewa, da kuma raya tsarin hadin kai tsakanin kasashen su, domin kara taka rawa wajen ingiza zaman lafiya, da kwanciyar hankali da wadata a shiyyar, har ma da dukkanin fadin duniya.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, yanzu ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, da ra'ayin bangaranci, suna kawo illa ga daidaiton tsarin duniya, kana sun kawo illa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, haka kuma sun kawo illa ga ci gaban kasashe masu tasowa. A don haka ya kamata kasashen Sin, da Rasha, da Indiya, su sauke nauyin dake wuyansu, domin kiyaye babbar moriyarsu, da moriyar daukacin kasashen duniya baki daya.

A nasa tsokaci, shugaban Rasha Putin ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, kamata ya yi kasashen Rasha, da Sin da Indiya, su yi kokari tare, domin kiyaye tsarin kasa da kasa, wanda ke karkashin jagorancin MDD, bisa tushen dokar kasa da kasa, tare kuma da kare ka'idar martaba 'yancin kasa, da ka'idar rashin tsoma baki a cikin harkokin cikin gida, da yin adawa da ra'ayin bangaranci, da ra'ayin ba da kariya, da kuma matakin sanya takumkumi bisa bangare guda.

Shi kuwa a nasa bangaren, firayin ministan Indiya Modi cewa ya yi, kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da ka'idojin kasa da kasa, ya dace da babbar moriyar kasashen uku, wato Indiya da Sin da kuma Rasha, don haka ya kamata kasashen su kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu a bangarorin gyaran fuska a fadin duniya, da bunkasa kwanciyar hankali a shiyya shiyya, da yaki da ta'addanci da dai sauransu. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China