Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da takwaransa na Amurka Donald Trump
2019-06-29 16:21:58        cri

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump a birnin Osaka na kasar Japan, inda suka yi musayar ra'ayi kan batutuwan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da takaddamar ciniki a tsakaninsu, da batutuwan kasashe da yankuna dake daukar hankalinsu, kana sun gabatar da shirin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin hadin gwiwa da zaman lafiya.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 40 da aka kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka, an samu babban canji kan yanayin duniya da dangantakar dake tsakaninsu, amma akwai wani batu da bai canja ko kadan ba, wato idan Sin da Amurka suka yi hadin gwiwa, za su samu moriyar juna, idan kuma suka nuna adawa da juna, sai za su samu hasara. Ya ce koda yake akwai wasu matsalolin dake kasancewa a tsakaninsu, moriyar bangarorin biyu suna dogara da juna, yana mai cewa, ana fadada hadin gwiwarsu, to ba za su ki amincewa da juna ba, ya kamata su sa kaimi ga samun bunkasuwa tare.

A nasa bangare, shugaba Trump ya bayyana cewa, bai nuna ra'ayin yaki da kasar Sin ba, yana fatan za a raya dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin yadda ya kamata. Yana da dora muhimmanci kan kiyaye yin mu'amala mai kyau tsakaninsa da shugaba Xi Jinping, kuma yana son kara hadin gwiwa tsakanin kasarsa da kasar Sin. Ya ce kasashen Amurka da Sin za su bi ka'idoji da hanyoyin da shugabannin kasashen biyu suka tabbatar da su, da yin aiki don raya dangantakarsu ta hadin gwiwa da zaman lafiya. Kana ya yi imani da cewa, ganawar dake tsakanin shugabannin Amurka da Sin a wannan karo za ta sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Game da batun tattalin arziki da cinikayya, Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta nuna sahihanci ga yin shawarwari da kasar Amurka, da daidaita matsalolinsu, amma ya kamata a yi shawarwarin cikin adalci da girmama juna. Game da batun dake shafar cikakken 'yancin da mutuncin Sin, ya ce tilas ne Sin ta tabbatar da kare moriyarta.

Shugaba Trump ya bayyana cewa, kasar Amurka tana fatan daidaita matsalar ciniki a tsakanin kasashen biyu ta hanyar yin shawarwari, da samar da dama cikin adalci ga kamfanonin kasashen biyu. Ya ce Amurka ba za ta kara buga sabon harajin kwastam ga kayayyakin da Sin ke shigarwa kasar ba. Yana fatan kasar Sin za ta kara shigar da kayayyakin Amurka cikin kasar. Har ila yau, ya ce Amurka tana son cimma yarjerjeniyar da bangarorin biyu suka amince da ita, wadda ke da babbar ma'ana. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China