2019-06-28 15:26:24 cri |
Ban da wannan kuma, shugaba Xi ya jaddada cewa, manufar yiwa kungiyar cinikayya ta duniya gyaran fuska ita ce, tabbatar da ganin kungiar ta samu damar bude kofar kasuwanni da sa kaimi ga samun bunkasuwa yadda ya kamata, kana ya kamata sakamakon da aka samu yayin kwaskwarimar, ya taimaka wajen kiyaye tsarin yin ciniki cikin 'yanci da kasancewar bangarori daban-daban da rage gibin bunkasuwa dake tsakanin kasashe daban-daban.
A cewarsa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" da Sin ta gabatar, na da burin shigar da karin kasashe da yankuna cikin tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya, don samun moriyar juna cikin hadin kai.
Dadin dadawa, shugaba Xi ya bayyana cewa, mambobin kasashen G20 sun samu bunkasuwa bisa matakansu, saboda haka suna da mabanbantan moriya da bambancin ra'ayi a tsakaninsu, ya kamata a yayata tunanin hadin kai da yin sulhu cikin adalci da samun bunkasuwa tare da amincewa da bambanci kan wasu batutuwa
Xi ya kara da cewa, Sin za ta gabatar da jerin sana'o'i da ayyukan da aka haramta zuba jari kansu a shekarar 2019, matakin da zai kara bude kofa ga ketare a fannin aikin gona, sana'ar hakar ma'adinai da samar da kayayyaki da sana'ar ba da hidima. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China