Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya gana da takwaransa na Afirka ta Kudu
2019-06-28 19:26:53        cri

A Yau Jumma'a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa, a birnin Osakar kasar Japan, inda shugaban na Sin ya jaddada cewa, ya dace kasashen biyu wato Sin da Afirka ta Kudu, su ci gaba da nuna goyon baya ga junansu a kan batutuwan dake shafar babbar moriyarsu, da muhimman harkokin duniya da suka fi jawo hankalinsu duka, kana su ci gaba da aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da hada shirye-shirye guda takwas da aka tsara, a yayin taron kolin Beijing, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da muradun raya kasa na gwamnatin Afirka ta Kudu a cikin shekaru biyar masu zuwa. Ban da haka kuma, su kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, a bangarorin samar da kayayyaki, da gina manyan gine-ginen more rayuwar jama'a, da raya albarkatun ma'aikata, da raya tattalin arziki ta yanar gizo, da raya fasahohin zamani da sauransu.

Xi ya yi nuni da cewa, kasarsa tana son kara karfafa cudanya, da hada kai tsakaninta da Afirka ta Kudu, domin kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya dake tsakanin bangarori daban daban, da aiwatar da adalci a fadin duniya, da kare moriyar kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu, da ma sauran kasashe masu tasowa.

A nasa bangare, shugaba Ramaphosa ya bayyana cewa, kasarsa tana matukar darajanta huldar abota dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana son kara karfafa cudanyar dake tsakaninta da kasar Sin, a bangaren gudanar da harkokin kasa, tare kuma da hada sha'anin raya kasarta da shawarar ziri daya da hanya daya waje guda. Ya ce hakika Afirka ta Kudu ita ma tana nacewa kan manufar zaman daidaito, da martabar juna, tare kuma da yin adawa da nuna ra'ayin bangaranci, da ra'ayin fin karfi, yayin da ake gudanar da cinikayyar kasa da kasa. Kana Afirka ta Kudu tana goyon bayan kasar Sin, wajen kiyaye hakki da moriyar ta na halal.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China