Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya ci gaba da halartar taron koli na 14 na kungiyar G20
2019-06-29 16:37:52        cri
Ana ci gaba da gudanar da taron koli na 14 na kungiyar G20 a birnin Osaka na kasar Japan, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarta.

Xi Jinping ya yi tsokaci game da batun samun bunkasuwa tare, ba tare da la'akari da bambance-bambance ba, inda ya yi nuni da cewa, Sin ta nuna goyon baya ga maida aikin gina ayyukan more rayuwa masu inganci a matsayin muhimmin aikin sa kaimi ga samun bunkasuwa ba tare da yin la'akari da bambance-bambance ba. Ya ce a kwanakin baya, an cimma daidaito da samun sakamako wajen raya shawarar "ziri daya da hanya daya" a gun taron tattauna hadin gwiwar kasa da kasa kan raya shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu da aka gudanar a nan birnin Beijing. Inda ya ce ya kamata a bi ka'idojin hadin gwiwa a fannonin cinikayya da raya kasa da kasa da more fasahohi, da tunanin bude kofa ga kasashen waje da kiyaye muhalli da yaki da cin hanci da rashawa, don cimma burin samun ci gaba mai inganci da dorewa da kuma samar da kyakkyawan zaman rayuwa ga jama'a. Ana fatan za a raya sha'anin samar da kayayyaki, da raya sana'o'i daban daban, da darajar kayayyaki ta hanyar yin hadin gwiwa don samun bunkasuwa tare. Xi Jinping ya ce, raya shawarar "ziri daya da hanya daya" wadda ta kasance dandalin hadin gwiwa na duniya mai bude kofa don amfanawa bangarori daban daban, za ta sa kaimi ga kasa da kasa su samun ci gaba tare. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China