2019-06-28 14:17:08 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20 da ta rungunmi damarmakin samun ci gaba, ta hanyar kara bude kofa da hadin gwiwar da za ta haifar da moriyar juna, domin daidaita alkibilar dunkulewar tattalin arzikin duniya bisa tafarkin da ya dace.
Xi Jinping ya yi alkawarin kasar Sin za ta kara bude kasuwarta da kara fadada shigar da kayayyaki kasar daga kasashen waje da ci gaba da inganta muhallin kasuwanci ga kamfanonin kasashen waje da kara kulla yarjeniyoyin cinikayya daban daban.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga taron kungiyar G20 dake gudana a birnin Osaka na kasar Japan. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China