2019-06-28 14:11:05 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, a yanzu yankin Gulf na cikin wani yanayi mai tsanani inda ya kasance a tsakanin yaki ko zaman lafiya.
Xi Jinping ya bayyana haka ne a birnin Osakan Japan, lokacin da yake ganawa da Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, gabanin taron kungiyar G20, ta kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.
Da yake tsokaci game da karuwar sarkakkiya da sabani da ake fuskanta a duniya, Shugaba Xi ya ce yankin Gulf na cikin wani yanayi mai tsanani, inda ya kasance a wata gaba dake tsakanin yaki da zaman lafiya
A nasa bangaren, Antonio Guterre ya ce yanayin kasa da kasa na cikin wani muhimmin lokaci, la'akari da bullowar takaddama a fannin cinikayya da kuma batun yankin Gulf, sannan duniya na fuskantar karancin karsashin inganta hadin gwiwar kasa da kasa da kiyaye dokoki da ka'idoji. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China