Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Sin da shugabannin kasashen Afrika dake halartar taron G20 sun cimma matsaya daya
2019-06-28 11:12:25        cri

Shugaban sashen kula da harkokin Afrika a ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Dai Bing, ya shaidawa taron manema labarai a cibiyar yada labarai ta kasar Sin a yau Jumma'a a birnin Osaka na kasar Japan cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da wani karamin taro da shugabannin kasashen Afrika a otel din da ya sauka. Wadannan shugabannin sun hada da shugaban Afrika ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa, da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, kasar dake rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka AU, da kuma shugaban kasar Senegal Macky Sall, kasar dake rike da shugabancin tawagogin wakilan kasashen Afrika a FOCAC, kana da babban magatakardan MDD Antonio Guterres.

Shugabannin biyar sun yi musanyar ra'ayi tare da cimma matsaya daya kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda yadda za a aiwatar da sakamakon da aka samu a taron koli na Beijing na FOCAC, da zurfafa hadin kan Sin da Afrika kan aikin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", kana da nuna goyon baya ga bunkasuwar kasashen Afrika da ayyukan MDD, da kiyaye tsarin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da aiwatar da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030 da dai sauransu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China