2019-06-28 14:37:53 cri |
Yayin ganawar, shugaba Xi ya gabatar da ra'ayoyi uku:
Na farko, ya kamata su ba da misali wajen samun bunkasuwa tare da kawo moriyar juna, ta yadda nasarorin da za su samu wajen hadin gwiwar za su amfanawa jama'ar Sin da Afrika.
Na biyu kuwa, kamata ya yi su jagoranci bude kofa da hadin kai, ta yadda za a tattara karfin raya nahiyar Afrika cikin hadin kai.
Na uku kuma, tilas ne su kare tsarin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, don ba da gudunmawarsu wajen kiyaye ka'idojin duniya.
Shugabannin Afrika mahalartan taron, sun bayyana cewa, taron da Sin ta shirya a wannan karo, ya bayyana muhimmanci matuka da Sin take dorawa kan kasashen Afrika. Afrika na godiya sosai kan gudunmawar da Sin take bayarwa don goyon bayan bunkasuwar nahiyar Afrika, da jinjinawa matakin kasar Sin na rashin tsoma baki kan harkokin cikin gidan sauran kasashe. Kasashen Afrika kuma na fatan hadin kai da kasar Sin don tabbatar da matakai 8 da aka cimma a gun taron koli na Beijing, da ba da himma da kwazo wajen raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma na al'ummar Afrika da Sin mai dankon zumunci. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China