Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya halarci taron shugabannin BRICS
2019-06-28 14:36:49        cri

An yi taron shugabannin BRICS a yau Jumma'a a birnin Osaka na Japan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Brazil Jair Bolsonaro, da na kasar Rasha Vladimir Putin, da na Afrika ta kudu Matamela Cyril Ramaphosa, da firaministan Indiya Narendra Modi, sun halarci taron. Yayin ganawar, shugabannin kasashen biyar sun yi musayar ra'ayi da kai ga matsaya daya kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda huldar kasashen BRICS, daidaita tsarin duniya, hadin kai kan aikin kirkire-kirkire da dai sauransu. Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro, kasar dake rike da shugabancin karba-karba na tsarin BRICS ne ya jagoranci taron.

Mista Xi ya nuna cewa, da farko, kara dankon zumuncin kasashen BRICS, na biyu kuma, kyautata matakin daidaita tsarin duniya. A ganinsa, ya kamata, kasashen BRICS sun nace ga matsayin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da kiyaye tsarin duniya bisa tushen dokoki da ka'idojin duniya, da kiyaye tsarin duniya bisa jagorancin MDD. Na uku, zurfafa hadin kai a dukkanin fannoni.

A nasu bangare kuwa, shugabannin mahalartan taro sun bayyana cewa, ya kamata kasashen BRICS su kara sulhuntawa tsakaninsu da ba da jagoranci yadda ya kamata, da kuma kiyaye tsarin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da kiyaye tsarin cinikayyar kasa da kasa bisa ka'idar da ta dace, da sa kaimi ga samar da adalci ga samun bunkasuwa da yin cinikayya mai dorewa bisa tushen mutunta juna. Ban da wannan kuma, kamata ya yi, a sa kaimi ga taron koli na G20 da su mai da muhimmanci kan samun bunkasuwa da tabbatar da alkwarin da aka yi na taimakawa nahiyar Afrika. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China