Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi da Abe sun cimma matsaya game da bunkasa alakar dake tsakanin kasashensu
2019-06-28 10:39:58        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Japan Shinzo Abe sun cimma matsaya game da bunkasa kyakkyawar alaka tsakanin kasashen su.

Shugabannin sun cimma wannan matsaya ce,yayin wata ganawa da suka yi gabanin taron kolin kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na duniya G20 da za a bude yau Jumma'a a birnin Osaka na kasar Japan.

Shugabannin biyu sun kuma amince su kara zurfafa alaka ta kare muradunsu kasashen da karfafa alakar moriyar juna a fannoni da dama kamar kimiya da fasahar kirkire-kirkire, da kare 'yancin mallakar fasaha da cinikayya. Sauran fannonin sun hada da zuba jari da harkokin kudi da kiwon lafiya da kula da tsofaffi, da tsimin makashi da kare muhalli da yawon shakatawa.

Shugaba Xi da firaminista Abe sun nanata cewa, kasashensu za su martaba turbar kiyaye zaman lafiya, da ma yin hadin gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Bugu da kari, shugabannin sun amince su kara yin tattaunawa kan yarjejeniyar cinikayyar Sin da Japan da Koriya ta kudu, za kuma su yi kokarin ganin an kammala sasantawa kan hadin gwiwar tattalin arzikin shiyya a cikin wannan shekara.

A madadin gwamnatin Japan, Mr. Abe ya gayyaci shugaba Xi don ya kawo ziyarar aiki kasar Japan a lokacin bazana na shekara mai zuwa, gayyatar da shugaba Xi ya amince da ita.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China