2019-06-27 19:41:11 cri |
A yammacin yau shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da firayin ministan kasar Japan Shinzo Abe a birnin Osaka.
Yayin tattaunawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata yana yin cudanya mai zurfi tsakaninsa da Shinzo Abe, a kokarin ciyar da huldar dake tsakanin Sin da Japan gaba yadda ya kamata, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Japan domin kara kyautata huldar dake tsakaninsu, ta yadda za ta dace da bukatun sabon zamanin da ake ciki.
Xi ya kara da cewa, yana sa ran shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 za su cimma matsaya wajen kiyaye tsarin tafiyar da cinikayya cikin 'yanci tsakanin bangarori daban daban, tare kuma da kara karfi ga ci gaban tattalin arzikin duniya.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China