Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na farko tsakanin Sin da Afrika
2019-06-27 14:09:59        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na farko tsakanin Sin da Afrika da aka bude yau Alhamis a Changsha, babban birnin lardin Hunan dake yankin tsakiyar kasar Sin.

Xi Jinping ya jaddada cewa, an kirkiro baje kolin wanda aka sanar yayin taron kolin Beijing na tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC) da aka yi a watan Satumban bara ne domin samar da dandalin zurfafa hadin gwiwar bangarorin biyu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.

Baje kolin tattalin arziki da cinikayya na farko tsakanin Sin da Afrika, ya hada gwamnatocin bangarorin biyu da masana da 'yan kasuwa da cibiyoyin hada-hadar kudi, domin tattauna manyan ayyukan hadin gwiwa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China