![]() |
|
2019-06-27 14:00:18 cri |
Shugaba Xi Jinping zai halarci taron kolin kungiyar G20 karo 14 ne bisa gayyatar da firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya yi masa.
A yayin taron, shugaba Xi Jinping zai kuma halarci kwarya-kwaryar tarukan da za a shirya tsakanin shugabannin kasashen BRICS da shugabannin Sin da Rasha da Indiya da kuma karamin taron da za a shirya tsakanin shugabannin Sin da Afirka. Baya ga haka, zai kuma gana da shugabannin kasashe da dama.(Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China