Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Congo Brazzaville: shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kawo moriya ga kasashe masu bin ta
2019-05-20 14:35:15        cri

Jakadan Congo Brazzaville dake kasar Sin Daniel Owassa ya bayyana a ranar 18 ga wata a nan birnin Beijing cewa, batutuwan yin mu'amala a tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka gudanar sun shaida cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" shawara mai kyau ce, ya kamata bangarori dake shawarar su kara yin hadin gwiwa da juna, da magance tasirin da sauran bangarori masu son lalata ta suka haifar musu.

Daya daga cikin bukukuwan murnar ranar samun 'yancin kai ta Afirka da aka shirya a ranar a nan birnin Beijing, ya hada da gasar wasan kwallon kafa ta sada zumunta a tsakanin jami'an diplomasiyya na Afirka da dalibai da malaman makarantun birnin Beijing kuma taron dandalin tattaunawa kan ra'ayoyin Sin da Afirka kan fannonin wasanni da bada ilmi, inda jakada Owassa ya halarci bikin tare da bayyanawa wakilin gidan rediyon kasar Sin CRI cewa, an raya dangantakar dake tsakanin Afirka da Sin yadda ya kamata. Kasarsa ta Congo Brazzavile da Sin abokai ne, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kara kawo sabbin nasarori ga hadin gwiwarsu, kamar yankin samar da kayayyaki na hadin gwiwa, da gina hanyoyin motoci da tasoshin mashigin teku da sauran ayyukan more rayuwa, wadanda suka taimaka ga samun ci gaba a kasashen biyu, tare da amfanawa jama'arsu baki daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China