Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya gana da wakilan jami'an gwamnatin da suka samu lambar yabo
2019-06-25 19:43:42        cri

Yau Talata a nan birnin Beijing, an gudanar da babban taron gabatar da lambobin yabo ga jami'an gwamnati da kungiyoyin jami'an gwamnati wadanda suka fi samun karbuwa daga wajen al'ummar kasar Sin karo na 9, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar, shugaban kasar kuma shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Xi Jinping ya gana da wasu wakilan da aka karrama a babban dakin taron jama'a, tare kuma da taya su murna, tare da fatan, za su ci gaba da yin kokari domin kara kyautata aikinsu na bautawa al'umma.

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma ministan ma'aikatar nada jami'an gwamnati Chen Xi shi ma ya gana da wakilan tare da shugaba Xi, inda ya bayyana cewa, jami'an hukumomin gwamnati suna taka muhimmiyar rawa yayin da ake kokarin tafiyar da sha'anin gina gurguzu, a don haka ya kamata daukacin jami'an kasar su yi koyi da nagartattun halayyen wadanda suka samu lambobin yabon, ta yadda za su kara ba da gudummowa a sabon zamanin da ake ciki.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China