Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bukaci matasan Sin da Japan da su bunkasa alaka tsakanin kasashen biyu
2019-06-26 19:48:33        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karfafawa matasan kasashen Sin da Japan gwiwa, da su rika ba da gudummawa, ta yadda za a samu kyakkyawar makoma ga hadin gwiwar kasashen biyu.

Xi ya bayyana hakan ne, yayin da yake ba da amsa a wasika da ya rubutawa Daichi Nakashima, matashin da ya lashe kofin Panda a gasar rubutun zube na matasan Japan, wanda ya rubutawa shugaban na kasar Sin wasika gabanin ziyarar da zai kai kasar Japan don halartar taron kolin kungiyar G20 a birnin Osaka.

A cikin wasikar, Nakashima ya mika sakon gaisuwa da fatan alheri ga shugaban kasar Sin, tare da bayyana kudurinsa na sadaukar da kai a kokarin inganta hulda tsakanin Sin da Japan.

A tasa wasikar, shugaba Xi, ya bayyana cewa, ya yi farin cikin ganin cewa, Nakashima ya dade yana karantar harshen Sinanci da al'adun Sinawa, kuma yadda ya shiga gasar rubutun zuben da ayyukan musaya a kasar Sin, ya koyi abubuwa da dama game da kasar Sin da kara kulla abota da abokai Sinawa.

Shugaba Xi ya yi fatan cewa, matasan kasar Sin da na Japan za su karfafa yin musaya da koyi da juna, karfafa fahimtar juna da kara kulla abota na har abada, da ba da gudummawa wajen samar da kyakkayawar makoma ga huldar dake tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China