2019-06-25 20:10:37 cri |
Yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Uganda Yoweri Museveni wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin, inda suka cimma matsaya game da daga matsayin huldar dake tsakanin kasashensu zuwa huldar sada zumunta ta hadin gwiwa daga dukkan fannoni.
Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, yanzu kasashen Sin da Uganda suna kara fahimtar juna a bangaren siyasa, haka kuma sun samu babban sakamako yayin da suke gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu, kasar Sin tana son ci gaba da hada kai tare da kasar Uganda domin ciyar da huldar dake tsakaninsu gaba ta hanyar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya da kuma tabbatar da nasarorin da aka cimma yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za su amfanin al'ummomin sassan biyu baki daya.
Xi ya jaddada cewa, ya dace Sin da Uganda su nuna adawa ga ra'ayin ba da kariya ga cinikayya da gudanar da harkokin cinikayya bisa bangare guda, haka kuma su kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD.
A nasa bangare, shugaba Museveni ya bayyana cewa, kasarsa tana fatan sassan biyu wato Sin da Uganda za su kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu yayin da suke kokarin kafa huldar sada zumunta ta hadin gwiwa daga duk fannoni, kana Uganda tana son kara karfafa cudanyar dake tsakaninta da kasar Sin a harkokin kasa da kasa.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China