Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya taya murnar taron tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin FOCAC
2019-06-25 11:26:26        cri
A yau Talata, aka gudanar da taron tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murnar kaddamar da taron.

Sakon ya nuna cewa, a watan Satumban bara, an gudanar da taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka a nan birnin Beijing, lamarin da ya kafa tarihi a huldar da ke tsakanin Sin da Afirka. Ya kuma yi farin cikin ganin cewa, Sin da Afirka na hada kansu wajen tabbatar da sakamakon da aka cimma a gun taron, tare da cimma wasu nasarori.

Shugaban ya jaddada a sakon cewa, a yayin da kasashe masu tasowa ke saurin bunkasa, yadda Sin da kasashen Afirka suke hada kansu zai iya samar da muhimmiyar gudummawa ta fannin kara karfin kasashe masu tasowa da raya sabon salon huldar da ke tsakanin kasa da kasa da kuma raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adam. Shugaban ya kuma yi fatan za a yi amfani da taron wajen yin shawarwari da tuntubar juna, don kara kawo alheri ga al'ummar kasashen Sin da Afirka biliyan 2.6.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China