Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka na fatan yin shawarwari da Iran ba tare da sharadi ba
2019-06-03 10:05:19        cri
Ministan harkokin waje na kasar Amurka Mike Pompeo wanda ke ziyarar aiki a Switzerland ya furta a ranar 2 ga wata cewa, Amurka na fatan yin shawarwari da Iran ba tare da sharadi ba, amma a cewarsa, Amurka za ta ci gaba da matsa wa kasar Iran lamba.

A gun taron manema labarai da ya gabatar tare da takwaransa na Switzerland Ignazio Cassis a wannan rana, inda ya ce, Amurka na yin shirin shawarwari da Iran ko da yaushe, amma Amurka ba za ta canja kokarin da take yi na tilasta Iran da ta canja matakin da take dauka ba.

Kafar yada labarai ta Iran ta ba da labari cewa, shugaban kasar Hassan Rouhani ya bayyana a ranar 1 ga wata cewa, Iran ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa tsoron irin matsin lambar da take mata ba. A cewar shugaban, idan Amurka tana son shawarwarin, to dole ne ta mutunta Iran da bin ka'idojin kasa da kasa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China