Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta yi watsi da kiran da Amurka ta yi mata na shiga tattaunawa ba tare da shadari ba
2019-06-04 11:33:34        cri

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce kiran da Amurka ta yi mata na neman shiga tattaunawa da ita tamkar wasa ne da hankali, kamfanin dillancin labarai na Tasnim shi ne ya bada rahoton a jiya Litinin.

"Bukatar da Washington ta nuna a baya bayan nan na cewa a shirye take ta shiga tattaunawa da Tehran ba tare da gindaya wasu sharruda ba tamkar wasa da hankali ne wanda ba za'a taba laminta ba," an jiyo Abbas Mousavi, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran din yana wannan furuci.

"Matakin da Amurka ta dauka na nuna aniyar shiga tattaunawa wani sabon salo ne da take nunawa game da hakikanin halin da kasar Iran ke ciki," in ji Mousavi, a martanin da ya mayar game da kalaman da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi kan batun tattaunawar da Iran.

Nacewar da mista Pompeo ya yi game da matsin lamba kan kasar Iran ya nuna cewa, Washington tana ci gaba da daukar mataki ne marar dacewa, wanda tun a baya take kansa, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China