Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran: Amurka ba za ta cimma burinta na kakabawa Iran takunkumi ba
2019-06-09 16:17:59        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta ba da sanarwar a ranar 8 ga wata tare da yin Allah wadai da sabon takunkumin da Amurka ke kakaba mata, a ganinta, Amurka ba za ta yi galaba ba game da matakin da take dauka na matsin lamba mafi tsanani kan Iran din.

Kakakin ma'aikatar Ayyed Abbas Almousawi, ya bayyana cikin sanarwar cewa, takunkumin da Amurka ta kakabawa kamfaninta na masana'antun man fetur na tekun Gulf ya sabawa dokar kasa da kasa, tamkar manufar ta'addanci ce kan tattalin arziki. Irin wannan takunkumi kasancewar yana daya daga cikin wasu matakan da Amurka ta kan dauka don nuna kiyayya kan kasar, matakin da ya sheda cewa, kiran da Amurka take yi na shawarwari da Iran ba gaskiya ba ne.

Sanarwar ta ce, duk wani mataki na matsin lamba kan Iran zai ci tura, bisa la'akari da matakan da shugabannin Amurka masu bari gado suka yi. Ya kamata kasashen duniya su yi Allah wadai da matakin da Amurkar ke dauka na kashin kanta da manufar babakere.

An ba da labari cewa, a ranar 7 ga wata, hukumar kudin Amurka ta ba da wata sanarwa cewa, kamfanin masana'antun man fetur na tekun Gulf na Iran yana ba da taimakon kudi ga kamfanonnin dake inuwar dakarun juyin juya hali na Iran IRGC, saboda haka, Amurka ta kakabawa kamfanin da rassansa 39 da sauran rassa dake ketare takunkumi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China