Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kamfanonin Amurka: Kara kakabawa kasar Sin haraji zai kawo illa ga kamfanoni da masu sayayya na Amurkawa
2019-06-18 14:02:39        cri
Ofishin wakilin cinikin Amurka ya kira wani taron sauraron ra'ayoyin jama'a mai raneku 7 a jiya Litinin, kan shirin da Amurka za ta gudanar wajen kara sanyawa kayayyakin da Sin ta ke shigarwa Amurkar harajin dala biliyan 300. Wakilan sana'o'i da kamfanoni fiye da 10 sun yi gargadi a taron cewa, matakin da Amurka za ta dauka zai sa kamfanoni da masu sayayyya na kasar hasarar, kuma zai rage karfin takarar Amurka da lahanta moriyar tattalin arziki da neman guraben aikin yi.

An ba da labarin cewa, wakilai kimanin 300 ne suka halarci taron da aka yi. Bayan taron, jama'a za su ba da shawarwarinsu ga ofishin wakilan cinikayyar Amurka a cikin mako daya. An ce, kafin wannan taro, kamfanoni 520 da kuma kungiyoyin ciniki 141 sun rubuta wata wasika cikin hadin kai ga shugaba Trump, don kalubalantar shugaban ya daina sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Sin da komawa teburin shawarwari da kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China