Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Duk zancen da Pompeo ya yi kan kasar Sin ba gaskiya ba ne
2019-06-10 20:20:03        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mista Geng Shuang ya bayyana a yau Litinin 10 ga wata a nan birnin Beijing cewa, a kwanakin baya bayan nan, ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya rika gabatar da jawabai duk lokacin da ya ga dama kan kasar Sin, amma kuma dukkanin irin wadannan abubuwan da yake fadi babu kanshin gaskiya a cikin su.

An ba da labarin cewa, yayin da Mike Pompeo ya zanta da manema labarai a Switzerland, ya bayyana cewa, da kyar ne kamfanonin kasar Sin za su iya kiyaye tsaron bayanai, kuma yin hadin kai da su tamkar hadin kai ne da gwamnatin kasar Sin. Game da hakan, Mista Geng ya bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana cewa, ko shakka babu "munafuncin dodo ya kan ci mai shi", wato dai duk karyace-karyacen da yake yi, suna rage mutuncin kasar Amurka a idon duniya ne. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China