Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takaddamar ciniki da Amurka ta tayar ta kawo illa ga ita kanta da kuma kasashen duniya
2019-06-13 13:49:19        cri

Dangane da wasu matakan nuna bangaranci da kuma bada kariya kan harkokin ciniki da gwamnatin kasar Amurka ta dauka a kwanan baya da kuma yadda ta tayar da takaddama ta hanyar kara dora kudin haraji, wasu jami'an kasashen waje da suka halarci harkar sashen yin cudanya da kasashen waje na kwamitin koli na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin sun bayyana a jiya Laraba cewa, kuskuren da Amurka ta yi ya kawo illa ga ita kanta da kuma kasashen duniya duka. Babu wanda ya amince da abubuwan da Amurka ta yi. Abubuwan data yi sun kawo illa ga duk duniya baki daya.

Ndinga Makanda, sakataren zartaswa na jam'iyyar 'yan kwadago ta kasar Congo (Brazzaville) ya bayyanawa manema labaru cewa, Amurka ta tayar da takaddama ne ta fuskar tattalin arziki da cinikayya kan kasar Sin da ma duk duniya baki daya. Yakin cinikayya ba kawai ya kawo cikas wajen raya huldar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Amurka ba ne, har ma ya kawo illa ga Amurka ita kanta, kuma zai iya haifar da karuwar rashin kwanciyar hankali a duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China