Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin waje na Sin ta nuna rashin jin dadi kan tsoma bakin da Amurka ta yi kan harkokin Hongkong
2019-06-15 16:03:39        cri

Mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng, ya gana da mukaddashin wakilin ofishin jakadancin Amurka dake kasar Sin Robert W. Forden cikin gaggawa, ya bayyana matukar rashin jin dadi kan zancen da Amurka ta yi kan wasu ayoyin dokar da yankin Hongkong yake aiwatar.

Mista Le Yucheng ya nuna cewa, yankin Hongkong na karkashin jagorancin babban yankin kasar Sin ne, harkokinsa ya kasance harkokin cikin gidan kasar Sin ne, babu wanda zai iya tsoma baki cikin harkokinsa. A 'yan kwanakin baya-bayan nan, wasu manyan jami'an Amurka sun yi ta yada jita-jita da tsoma baki kan gyaran dokar da Hongkong ya yi kan wasu ayoyin dokar yankin, Sin ta nuna bacin ranta sosai kuma ba za ta yarda ba ko kadan. Kana kasar Sin tana kalubalantar Amurka da ta kyautata tunaninta kan lamarin cikin adalci, da mutunta ikon gwamnatin yankin Hongkong na gyara dokarsa wanda ake gudanar da shi yadda ya kamata, da daina tsoma baki kan harkokinsa, kada ta dauki ko wani mataki da zai iya kawo illa ga zaman wadata mai karko na yankin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China