Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka ba za su katse huldar dake tsakaninsu ba
2019-06-12 20:13:33        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Gengshuang, ya musanta korafin da wasu Amurkawa suka yi, cewa wai Sin da Amurka za su katse huldar dake tsakaninsu, inda ya nanata cewa, wadannan mutane masu bahaguwar fahimta ne dake hangen yiwuwar dorewar cacar baka, kuma a ganinsu babu yiwuwar hadin kai, da samun moriyar juna tsakanin sassan biyu.

Jami'in ya ce wannan tunani ne na masu raunin imani, kuma ya sabawa manufar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, game da hadin kai da samun moriyar juna, ya kuma yi biris da dankon zumunci dake akwai tsakanin jama'ar kasashen biyu, kana ya sabawa bunkasuwar zamani, don haka dai ba wanda zai amince da shi ko kadan ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China