Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Duk wani yunkuri na tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar Sin zai ci tura
2019-06-11 20:31:41        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mista Geng Shuang ya bayyana yau 11 ga wata a nan birnin Beijing cewa, ko kadan ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ba shi da ilmi game da jihar Xinjiang ta kasar Sin. Kuma manufarsa ta fito fili daga irin jawaban da yake yi a baya-bayan nan.

Rahotanni sun nuna cewa, a kwanakin baya-bayan nan Pompeo ya furta wasu kalamai game da jihar Xinjiang, inda ya yi zargin cewa, wai gwamnatin kasar Sin ta tsare musulman kananan kabilu a kalla miliyan 100, don tilasta musu yin karatu, matakin da ta dauka a tsawon lokaci, ya hana musulman yin addininsu bisa zabin zuciyarsu.

Game da wannan karya, yayin taron manema labarai na yau Talata, Geng Shuang ya ce, "gani ya kori ji", karairayin da Pompeo ke furtawa, sun shaida cewa, ba shi da wani ilmi, ko sani ko kadan game da jihar ta Xinjiang.

Ban da wannan kuma, Geng ya ce, Sin ta nemi Amurka da ta gyara tunaninta, game da gyaran doka da yankin Hongkong ya yi, kan wata ayar dokar yankin, ta kuma daina daukar ko wani irin matakin tsoma baki kan harkokin Hongkong, da ma sauran harkokin cikin gidan kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China