2019-06-13 19:52:06 cri |
Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mista Gao Feng, ya bayyana a yau Alhamis a nan birnin Beijing cewa, ko kadan kasar Sin ba ta yarda da manufar gudanar da harkoki bisa ra'ayin kashin kai, da matakin babakere da Amurka ke dauka ba.
A cewarsa, "Sin ba ta son yin kafsawa da kowa, amma idan hakan ya zama wajabi, ba za ta ji tsoro ba". Ya ce idan Amurka ta kara tsananta takaddama tsakanin bangarorin biyu kamar yadda take son, to Sin za ta mayar da martani.
Gao Feng ya kara da cewa, Sin ba za ta ja da baya ko kadan kan wasu manyan batutuwan da suke shafar babbar moriyarta ba, saboda tana nacewa ga matsayin hadin kai bisa ka'ida, da gudanar da shawarwari bisa muhimman burikan ta. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China