Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afrika na da kyakkyawar dama ta hadin kai a fannin kiyaye kayan tarihi na al'adu
2019-06-05 11:02:48        cri

Mataimakin ministan hukumar kiyaye kayan tarihi na kasar Sin Mista Song Xinchao ya shedawa manema labarai jiya a birnin Paris cewa, Sin da Afrika na da dogon tarihi da al'adu mai kayatarwa, kuma kayan tarihi na al'adu na sheda mafari da bunkasuwar al'adun Bil Adama, kuma bangarorin biyu na fuskantar kalubale da wahalhalu da dama wajen kiyaye kayan tarihi na al'adu.

Mista Song ya ce, Sin da Afrika na fuskantar matsalar daidaita dangantakar raya tattalin arziki da kiyaye kayan tarihi tare. Kuma yawan amfani da albarkatun halittu, da karancin tsare-tsare da rashin samun jagoranci a sha'anin yawon shakatawa, da illar da ayyukan gine-gine ke kawowa kayan tarihi da dai sauran matsaloli, na kawo cikas sosai ga samun bunkasuwa mai dorewa.

Mista Song ya kara da cewa, Sin da Afrika na da dadadden tarihin zumunci, wanda bangarorin biyu ke kara inganta shi a shekarun baya-baya nan, la'akari da yadda suke tuntubar juna sosai a wannan fanni. Ya zuwa yanzu, Sin ta sa hannu kan shirin hadin kan gwamnatoci ta fuskar al' adu da shirin gudanarwa da kasashen Afrika har 52, wanda ke kunshe da aikin kiyaye kayan tarihi na al'adu. Ban da wannan kuma Sin ta kulla yarjejeniya da Habasha, Masar, Nijeriya da dai sauransu, kan yaki da haramta sufuri kayan tarihi tsakanin kasa da kasa. Kana kuma Sin ta hada kai da masana nazarin kayan tarihi na Afrika don yin bincike a yankin wurin ibada na Karnak na Masar da tsibirin Lamu na Kenya. Haka zalika, Sin ta ba da taimako wajen horar da masana kimiyya daga Afrika a wannan fanni, ta hanyar ba da kyautar kudin karatu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China