2019-06-02 12:14:16 cri |
Illar da matakan suka kawowa kasar Amurka sun hada da kara yawa kudin samar da kayayyaki na kamfanonin Amurka, da daga farashin kaya na kasar, da ma kawo tasiri ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar da zaman rayuwar jama'ar kasar, da kawo cikas ga fitar da kayayyakin Amurka zuwa kasar Sin. Bisa rahoton da kungiyar ciniki ta kasar Amurka da sauran kungiyoyin kasar suka gabatar, an ce, idan kasar Amurka ta kara kudin harajin kwastam da kashi 25 cikin dari kan dukkan kayayyakin Sin da ake fitar da su zuwa kasar Amurka, sai yawan GDP na kasar Amurka na shekaru 10 masu zuwa zai rage da kudin Amurka dala triliyan 1. (Zainab)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China